Kowa da matsalarsa: Matashi ya kama hanya a kasa don jinjina ma Sarkin Kano Aminu daga Jigawa

Posted by Martina Birk on Friday, August 9, 2024

Wani matashi mai ji da kardi daga jahar Jigawa ya kaddamar da tattaki zuwa jahar Kano domin taya sabon Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero murnar darewar karagar mulki.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan matashi mai suna Umar dan asalin jahar Kano ne, amma yana karatu a jami'ar gwamnatin tarayya dake birnin Dutse na jahar Jigawa.

Murna da farin ciki da ya turnuke Umar biyo bayan sanar da Aminu Ado a matsayin sabon Sarkin Kano ne yasa ya fara wannan tattaki domin yin jinjinar ban girma, tare da bayyana ma sabon sarkin farin cikinsa da kuma fatan alheri.

KU KARANTA: Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

Gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

Sai dai tuni gwamnatin ta sanar da tsohon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano, yayin da dan uwansa Nasiru Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Bichi.

Nadin Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano ya samu amincewar manyan fadawan masarautar Kano guda hudu wadanda suka isa fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Litinin domin tattaunawa da Gwamna Ganduje kafin sanar da sunan sabon Sarkin Kano.

Manyan masu nadin Sarkin sun hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Abdullahi, Sarkin Dawaki Mai Tuta Abubakar Tuta da Sarkin Bai Mukhtar Adnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kmpna2lnYriww8Bmm5plnZbBtK3LmqmsmV2irrWt0qGgZrGRYriiucBmn5qmqZZ6onnKmqqaZZSku262yKehoqaRYrqiedKaqaShnmK4orrOZpimoZ6qeqWtxppko6GXlsSiesetpKU%3D